Wani tarin manhajoji na kyauta, masu harsuna da dama, wadanda ke aiki ba tare da kafar sadarwa ta yanar gizo. An gwada su a cikin al’umma, kuma Hesparian tana ba da muhimmanci ga kare sirri.
Manhajar lafiyar ciki da haihuwa tana ba da sahihiyar bayanai cikin sauki da fahimta game da ciki, haihuwa da kulawa bayan haihuwa. Hotuna masu bayani da amfani da saukaken harshe sun sa wannan manhaja mai lambar yabo ta zama mai amfani ga ma’aikatan lafiya da suke aiki a karkashin al”umma, unguwar-zoma, da dai-daikun mutane da iyalansu. An kirkire ta domin saukin saukewa, tana da cikakken amfani kuma kyauta ce. Wannan manhajar tana aiki ko da babu kafar sadarwa ta yanar gizo ko kuma data.
.
Za ka iya duba dokar sirrin manhajar wayarmu anan
(da Turanci ko Sifaniyanci)
Amfani da manhajar ta kafar sadarwa ta yanar gizo
Yana kunshe a manhajar rainon ciki da haihuwa:
-
Zama cikin koshin lafiya alokacin da ake da juna biyu, yaya za ki ci abinci me kyau, abubuwan da zaku duba alokacin ciki, yaya za’a kula da tashin zuciya da sauran korafe-korafe.
-
A tabbatar da haihuwa lafiya, da kayan da za a tanada kafin haihuwa, yadda za a taimaka a kowane mataki na nakuda, gane alamomin gargadi da lokacin da ake bukatar kulawar gaggawa
-
kulawa bayan haihuwa – yadda za a kula da jariri da iyaye nan da nan bayan haihuwa, da kuma cikin makon farko,harda ciwon damuwa na masu haihuwa da kuma tallafa mata wajen shayarwa.
-
Yaya za,a bada bayani –samun bayanai cikin sauri kan muhimman kwarewar kula da lafiya bisa jigo
-
Kalkuleitar mata masu juna biyu














