Manhajar Tazarar Haihuwa App
Jerin manhajoji na kyauta, masu harsuna da yawa, wadanda suke aiki ba tare da yanar gizo ba.
Al’ummomi sun gwada amfani da ita, Manhajojin Hesperian sun fi ba da fifiko wajen tsare sirrin masu amfani da su.
An kirkiri wannan manhaja ne domin Ma’aikatan lafiya na matakin farko, Shugabannin al’umma, matasa masu jan ra’ayin sa’anin su, wannan manhajar cike take da ingantattun hotuna da zane-zane, dauke da bayanai masu saukin fahimta, da kayan aikin hadin gwiwa don taimakawa tattaunawa game da lafiyar haihuwa. Tazarar haihuwa na kunshe da muhimman batutuwa don yin nasiha ciki harda da yadda ake amfani da kowace hanya, yadda yake hana samun juna biyu, yadda za a iya boye shi cikin sauki, da kuma illolinsa.
Yi amfani da manhajar a yanar gizo!
Kunshe a cikin manhajar tazarar haihuwa:
-
Hanyoyin maganin tazarar haihuwa – Bayanai game da hanyoyin kariya, dabi’ance, masu sinadarin hormones, da hanyoyin dindindin tare da ingancinsu, amfaninsu, da rashin amfanin kowannensu.
-
Zaben Hanyoyi – kayan aikin da ke taimakawa masu amfani gano hanyoyin maganin tazarar haihuwa da ta dace da zabin su da salon rayuwarsu , da tarihin lafiyasu.
-
Tambayoyin da ake yawan yi (FAQs) – amsoshin galibin tambayoyi game da maganin tazarar haihuwa da kuma damuwar da aka fi samu akan hanyoyin takamaimai, kamar ko ana iya sake amfani da kwaroron roba, da lokacin da za a fara amfani da kowace hanya bayan haihuwa, yin bari ko zubar da ciki.
-
Dabaru da misalan ba yin nasiha – nganta kwarewarka wajen ba da nasiha, jin dadinka na tattauna batutuwan da suka shafi lafiyar haihuwa, da iyawarka na tallafa wa mutane daga nau’o’in al’adu daban-daban da matakan rayuwa daban-daban.










